Wani matashi mai shekaru 15 mai suna Kabiru Idi ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jahar Niger a sakamakon kama shi da aka yi ya na lalata da akuya.
An kama Idi wanda dan asalin kauyen Gbeganu ne a karamar hukumar Bosso a jahar bayan da wasu mutane suka tseguntawa ‘yan sanda abunda ke faruwa.
Rahotanni sun nuna cewa karo na biyu kenan da matashin ke aikata irin wannan laifi.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar, Babalola Adewole ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce jami’an su na yankin Kpakungu ne suka cakfo matashin a yayin da suka fita sintiri.
Ya ce za a gurfanar da shi a gaban kuliya da zaran an kammala bincike.
Ya kuma yi kira ga jama’a da kar su yi kasa a gwiwa wajen kai masu rahoto da zaran sun ga wani abunda ba shikenan ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a da kar su yi kasa a gwiwa wajen kai masu rahoto da zaran sun ga wani abunda ba shikenan ba.
No comments:
Write comments