whatsapp:

+2348100509931

Gmail: Nazeerhacker560@gmail.com

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Thursday, 7 September 2017

Neman Aure: Wani Ya Rasa Ransa a Jihar Katsina a Gasar Sharo na Neman Aure


                          ©Alummata

Wani mai suna Yari Inusa ya rasa ransa a yayin da shi da wani Ahmad Sa’idu suka kara a gasar sharon da zai baiwa wanda ya yi nasara damar auren wata budurwa

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Durumin Biri da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina

‘Yan sanda a karamar hukumar Kafur sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka bayyana cewa gasar neman auren wata yarinya ya sanya Yari Inusa shiga gasawasan sharo da Ahmadu Sa’idu

Lamarin ya baci ne bayan da Yari ya kammala tsalawa Ahmadu bulala, amma Ahmadun bai yi ko gezau ba. Sai dai Ahmadun na zabgawa Yari tsumagiyar, sai Yari ya fadi kasa warwas a sume

Shaidun gani da ido sun zargi Ahmadu da zabgawa Yari tsumagiyar a bayan kansa, wanda hakan ya yi sanadiyyar sumar da Yari, inda daga bisani kuma ya ce ga garinku nan

No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter NAZEER YOUNG-HACKER
Join Our Newsletter